BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Haidar Ali
KARATUN MALAM ZAKZAKY (H) DA HAZAKARSA
(BABI NA UKU)
Bayan kuma Malam (H) ya je kano. Kamar yadda na soma bayani. Ya kasance mai matukar hazakar da sauran dalibai ke sha'awar Neman Karin fahimtar karatu daga wajensa.
A lokaci daya kuma akwai wadansu dalibai wadanda sukayi kokarin su cimma masa a bangaren hazaka da kuma kokari a aji. Amma kuma alokacin duk da suka kokar ta. Akarshe za'a tarar da cewa Malam (H) ne ke kan gaba. A ko dayaushe Malam ne ke rinjaye, Ba Wanda ke iya ja-in-ja da Malam a fagen hazaka da kokari. Shine kuma yake samun sakamako n farko ako da yaushe .wannan kuma awani bangare. Ya haifar ma Malam (H)
mashahuriyyar daukaka a stakanin shuwagabannin makarantar. Musamman malamai. Akodayaushe malamai sunaso suji ra'ayin Malam (H) akan wata tambaya da suka yi. Koda kuwa ba Malam (H) sukayi wa tambayar ba. Ako da yaushe Malam (H) ke kan gaba.
Antaba shirya wata ga sar rubutu a makarantar SAS kano da turanci kan jahiliyya kafin bayyanar musulunci malam (H) yazo na daya a gasar.harma mataimakin shugaban makarantar na lokacin -wani malami mai suna Malam datti Ahmad yanuna cewa wannan rubutun na malm (H) shine iyakar abinda Malam zai rubutu ta koda kuwa a shekarar kar she nakaratun sa ce.
Har kuma shi mataimakin shugaban makarantar yasa aka buga rubutun na Malam (H) aka kuma rarrabawa dukkanin ma aikatan makarantan. Malamai dakuma sauran dalibai Haka ma ko a jami'ar Ahmadu Bello, Malam yanuna basira dakuma hazakar da Allah (S W T) ya hore masa ainun a lokacin kammala karatun Malam (H) a jami'ar ya samu sakamako mai daraja ta farko wato sakamako mafi daraja. Abin da za mu Dan kara a wannan rubutu shine Malam allah ya hore masa wata baiwa ta mashahuriyar basira da hazaka da kuma kwakwalwa wadda tasha bambam Dana sauran mutane. Wannan baiwar ta Malam itace tasa cewa shi ko da kadan ne yayi karatu. Sai kaga Allah (S W T) ya fahimtar da shi da yawa.
Anshedi Malam da wannan tun yana yaro wato Allah ya hore ma Malam fahimta mai zurfi. Malam (H) yana yiwa karatun dayayi kadan fahimata wadda ko da Wanda ya dauki shekaru masu yawa yana karatun baya fahimta. Wannan kadan kenan daga cikin hazakar Malam (H) wadda aka kiyaye a lokutan karatunsa na tsakanin Zaria da kuma kano.
sa'annan kuma daga baya Malam (H) yayi karatu na Dan gajeren lokaci a jumhuriyar musulunci ta Iran kusan shekaru goma da suka wuce a wancan lokacin amma kuma fahimtar da ya yiwa karatun ta ma fi ta wadanda su kayi shekaru suna karatun.tun daga lokacin ne kuma yake ta bincike-bincike na ilimi a inji mai kwakwalwa. Wato kwamfuta,
kadan daga cikin malaman Malam (H) Malam yayi karatu a wajen malamai masu daman gaske a stakanin yarintarsa zuwa samartaka.da kuma lokutan karatunsa na birnin zariya da kuma kano.wasu kadan daga cikin malaman Malam (H) a birnin zariya suna hada da
●Malam sani abdulkadir
●Malam isa na madaka
●Malam sani na'ibi
●Malam Ibrahim kakaki
Da sauran su da dama
A birnin kano kuwa kadan daga cikin malaman da suka karantar da Malam Ibarhim Zakzaky (h)
●Malam Nasiru kabara
●Malam isa waziri
●Malam Nuhu limami
●Malam datti ahmad
●Malam abdulra'uf usman (mutumin masar)
Da dai sauransu da dama
Wadannan kadan kenan daga cikin malaman Malam (H) a lokacin da yayi karatunsa na stakanin birnin zariya da kano
_ALHAMDULILLAH_
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved